Gwamnatin Jigawa ta kaddamar da rabon motoci ga Shugaban Makarantar Sakandire

0 610

Kwamishinan Maaikatar Iilmi Mai Zurfi ta jihar Jigawa, Farfesa Isa Yusif Chamo ya kaddamar da rabon motoci ga shugabannin manyan makarantun Sikandare na jihar nan.

Da yake mika makullan motocin ga wasu shugabannin makarantun sikandaren jihar guda biyar, Farfesa Isa Yusuf ya ce wannan shine kashin farko na rabon motocin ga shugabannin makarantun sikandare domin samun saukin gudanar da aiyukansu.

Ya ce basu motocin zai basu kwarin gwiwa wajen gudanar da aiyukansu.

Farfesa ya kara da cewar an kuma bada Babura ga ofisoshin shiyya shiyya na maaikatar domin baiwa jamian shiyyar damar yin zurga zurga zuwa makarantu.

Kwamishinan yana mai cewar maaikatar ta kashe kudi naira miliyan dari da ashirin wajen sayen motocin da kuma baburan.

An raba motocin ne ga shugabannin makarantun sikandare na Bamaina da Dutse model da sikandaren kimiyya ta Kafin Hausa da makarantar koyan sana-a ta Garki da kuma sabon shugaban hukumar lura da manyan makarantun sikandare na jihar.

Leave a Reply