Hukumar NDLEA ta jaddada kudirin ta na yaki da masu amfani da kuma sayar da miyagun kwayoyi a jihar Jigawa

0 145

Hukumar hana sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta jihar Jigawa ta jaddada kudirin ta na yaki da masu amfani da kuma sayar da miyagun kwayoyi a jihar nan.

Kwamandan hukumar na jiha, Malam Musa Maina ne ya bayyana haka lokacin ganawa da manema labarai a wani bangare na bikin ranar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta duniya.

Ya ce yaki da miyagun kwayoyi abu ne da ake gudanar da shi a kowacce rana, inda hukumar ta yi nasarar kwace miyagun kwayoyi da adadin su ya kai nauyin kilogiram dubu daya da dari uku daga watan afrilu zuwa yau.

Malam Musa Maina ya godewa sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin da masu yiwa kasa hidima da kuma dalibai da suka bada gudunmawa a lokacin gudanar da wannan biki.

A nasa jawabin shugaban kwamatin yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi na jiha, Alhaji Khadi Bashir Birnin kudu ya ce manufar bikin shine domin wayar da kan jama’a illar dake tattare da ta’ammali da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Ya yi kira ga jama’a da su guji amfani da miyagun kwayoyi ko kuma sayarwa domin samun lafiya a tasakanin al’umma.

Tun da farko hukumar ta gudanar da zagaye a cikin kwaryar Dutse domin fadakar da al’ummakan illolon miyagun kwayoyi.

Leave a Reply