Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa cutar amai da gudawa wato kwalara ta kashe akalla mutane 20 a jihar.

0 199

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa cutar amai da gudawa wato kwalara ta kashe akalla mutane 20 a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aliyu Maigoro ne ya bayyana hakan a yau a wani taron manema labarai da ya kira a hedikwatar ma’aikatar da ke Bauchi.

Yace kananan hukumomi 9 a jihar sun samu jimillar mutane 322 da suka kamu da cutar a wata daya inda ya kara da cewa yawan mace-macen ya kai kashi 6.2 cikin 100.

Yace ma’aikatar ta hannun Hukumar Bunkasa Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta hanzarta kai dauki don hana yaduwar cutar zuwa sauran kauyuka da unguwanni, inda ya kara da cewa an gano cewa akwai bullar irin wannan cuta a karamar hukumar Sumaila dake makotaka da sauran Kananan Hukumomin Jihar Kano.

Aliyu Maigoro ya ce tuni aka kaddamar da cibiyoyin kula da cutar kwalara guda hudu a cikin garin Bauchi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, da Asibitin Kwararru na Bauci, da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Matasa da kuma Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko dake Kandahar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: