Abokin Messi, Luis Suares ya rokeshi da ya ci gaba da zama a Barcelona

0 230

Tauraron dan wasan Uruguay kuma da ke taka leda a Atletico Madrid Luis Suarez matsayin dan wasan gaba, ya roki Lionel Messi na Barcelona da kada ya bar kungiyar, inda yake cewa zai yi matukar farin ciki idan kaftin din Argentinan ya cigaba da zama a kungiyar sa.

Suarez wanda ya lashe gasar La Liga da kungiyar Atletico Madrid bayan da Barcelona ta kore shi bara, ya ce fatar sa ita ce ganin Messi ya ci gaba da yi wa Barcelona wasa ganin cewar ita ce kungiyar da ya ke wakilta a rayuwar sa ta shahararen ‘dan wasa.

Dan wasan ya ce a matsayin sa na aboki kuma mai sha’awar wasan Messi, zai yi matukar farin ciki idan dan wasan Argentinan ya ci gaba da zama a kasar Spain, saboda irin kima da darajar da ya kawowa kungiyar Barcelona da kuma yadda ita ma kungiyar ta daga darajar sa.

Kafofin yada labaran Spain sun bayyana cewar Messi na bukatar sabuwar kwangila a Barcelona, amma Suarez da suka ci abinci ya bayyana shakku akai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: