Gwamnatin jihar Borno ta bayyana barkewar cutar kyandar-biri a jihar tare da samun mutum uku a cikin wadanda NCDC ta tabbatar

0 99

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana barkewar cutar kyandar-biri a jihar tare da samun mutum uku a cikin wadanda, Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC), ta tabbatar da cewa suna dauke da cutar.


Daraktan kula da lafiyar al’umma a Ma’aikatar Kiyon lafiya a jihar, Dakta Lawi Mshelia, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin.

Ya ce, “Bayanan samun mutum biyu wadanda suke dauke da cutar ya zo ne bayan gwajin da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ya gudanar, wanda yanzu haka suna ci gaba da samun kulawar likitoci, sannan sauran kuma sun fito ne daga karamar hukumar Biu da ke kudancin jihar Borno.”
Bugu da ƙari, Daraktan ya bayyana cewa an sallami ɗaya daga cikin majinyatan a makon da ya gabata.


A hannu guda kuma, Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar da gangamin wayar da kan jama’a domin ganin sun ɗauki ingantattun matakan kariya daga kamuwa da cutar kyandar-biri, kwalara da cutar COVID-19.


Babban jami’in WHO mai kula da ayyukan gaggawa kan cututtuka masu saurin yaduwa a Arewa Maso Gabas, Dakta Richard Lako, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ƙoƙarin hukumar na faɗakar da al’umma kan cututtuka masu yaduwa.


Dakta Lako ya bayyana cewa, “Abu ne mai matukar muhimmanci wanda za mu yi aiki tuƙuru wajen ganin kowa ya karɓi alluar riga-kafin cutar Korona.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: