Gwamnatin jihar Jigawa hadin gwaiwa da jami’an tsaro na aiki tukuru domin dawo da zaman lalfiya a Guri – Alhaji Musa Sha’aibu

0 95

Awani labarin kuma shugaban karamar hukumar Guri Alhaji Musa Sha’aibu Muhammad ya ce karamar hukumar Guri, da gwamnatin jihar Jigawa hadin gwaiwa da jami’an tsaro na aiki tukuru domin dawo da zaman lalfiya a fadin karamar hukumar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin daya karbi shugabannin kungiyyar Hadejia Ina Mafita, a lokacin da suka kai masa ziyarar jaje a ofishinsa dake Guri.

Biyo bayan yamutsu da aka samu tsakanin Fulani makiyaya da manoma.

Shuaibu ya kuma bukaci mutanen karamar hukumar da su guji yada labaran karya wanda yake haifar da fitina a cikin al’umma.

Anasu bangaren shugaban kungiyyar Hadejia Ina Mafita Dr Usaini Shehu da kuma sakataren kungiyyar Alhaji Salisu Muhammad Birniwa sun bukaci masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani da su kasance masu taka tsan-tsan wajan yada ra’ayoyin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: