Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada sakon ta’aziyya da kuma jaje ga wadanda suka mutu da kuma jikata sanadiyyar rikicin Fulani da manoma a karamar hukumar Guri

0 99

Gwamnatin jihar Jigawa ta aike da sakon taaziyya da kuma jaje ga wadanda suka Mutu da kuma Jikata sanadiyyar rikicin Fulani da Manoma a karamar Hukumar Guri.

Mataimakin Gwamnan jiha Mallam Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar jajen fadar mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje a madadin gwamnan jiha Muhammad Badaru Abubakar.

Yace gwamnan ya nuna alhini dangane da abin da ya faru tare da bada tabbacin gwamnatin jiha na gudanar da bincike domin kawo karshen rikicin Fulani makiyaya da manoma a yankin Guri da ma kasa baki daya.

Mallam Umar Namadi ya ce gwamnati zata gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin da kuma daukar matakan da suka dace.

Inda suka bukaci Fulani makiyaya da manoma dasu cigaba da zama lafiya da junansu, yana mai cewar babu wani cigaba da za a samu muddin babu zaman lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: