

Akalla mutane 20 ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Ganar-Kiyawa da ke gundumar Adabka a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.
Harin na baya-bayan dai ya faru ne a jiya da safe inda ‘yan bindigar suka afkawa al’ummar garin inda suka fara harbe-harbe kai tsaye, tare da kashe mutane 20 ciki har da mai unguwar.
An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kuma kai hari a wasu kauyukan da ke yankin, inda suka yi awon gaba da shaguna tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja
Wata majiya daga yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce al’ummomin da ke karkashin gundumar Adabka sun sha fama da hare-hare da sace-sace daga ‘yan fashin.
Ya kuma ce mazauna Ganar Kiyawa suna kwana a cikin daji saboda tsoron kada ‘yan bindiga su kai musu hari a gidajensu.
Da aka tambaye shi game da martanin da hukumomin tsaro suka mayar, ya ce sojoji sun tsaya ne kawai a Adabka da garin Gwashi, lamarin da ya sa wasu kauyukan suka fuskanci hare-haren ‘yan bindiga.
Amma harkawo lokacin hada muku wannan rahoton hukumomin ‘yan sanda a jihar har yanzu ba su tabbatar da sabon harin ba.