Gwamnatin jihar Jigawa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin Europa Carbon Limited, wani kamfanin makamashi, a wani gagarumin yunkuri na magance sauyin yanayi da kuma bunkasa kudaden shiga na jihar.
An gudanar da bikin sanya hannun a ranar Litinin a gidan gwamnati da ke Dutse, inda gwamna Mallam Umar Namadi ya jagoranci taron.
Manajan Darakta/Shugaba na Europa Carbon Limited, Engr. Muhammad Yadudu, ya jagoranci tawagar kamfaninsa zuwa bikin.
Yadudu ya ce, “Wannan yarjejeniya tana wakiltar wani muhimmin bangare na dabarun gwamnatin jihar na rage fitar da iskar Carbon, da karfafa juriyar yanayi, da inganta ci gaba mai dorewa. A karkashin yarjejeniyar za a samar da makamashi mai tsafta domin tallafawa ayyukan noma da masana’antu a fadin jihar Jigawa.”
Gwamna Namadi ya bayyana c ewa yarjejeniya za ta taimaka wajen rage fitar da gurbatacciyar iskar, da habaka kudaden shiga, da kuma ba da gudummawa wajen samar da tsaro da tsaftar Jigawa.” Gwamna Namadi ya kara da cewa “Wannan yarjejeniya na daya daga cikin manufofi guda 12 na gwamnsatinsa don inganta kudaden shiga.