Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyana cewa, ruwan sama da ambaliya ya yi barna a fadin kasar nan,wanda ya bazu zuwa jihohi 28, da ya yi sanadin mutuwar mutane 175, yayin da wasu dubu 207, 902 suka rasa muhallansu.
Hukumomin kasar sun bukaci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su kaura zuwa wasu matsuguni yayin da ake ci gaba da samun ruwan sama, biyo bayan gargadin da hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi game da mamakon ruwan sama, inda ta bukaci a shirya domin fuskantar ambaliyar ruwa.
An tattaro cewa gwamnatocin jihohin tare da hadin gwiwar hukumar NEMA, sun fara yunkurin kwashe mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa.
Shugabar hukumar ta NEMA, Zubaida Umar, ta kara da cewa hukumar ta bude cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kasa sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a kwanakin baya.
Jami’in hukumar ta NEMA ya ce, ambaliyar ruwa a kasar ba daga koguna bane amma galibi ana samu ne daga ruwan sama. Shugaban kasa Bola Tinubu ya jajanta wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kasar, ya kuma kuduri aniyar bayar da tallafin da ya dace don ganin an farfado da su daga barnar da ta shafe su.