Gwamnatin jihar Jigawa ta bada tabbacin tallafawa sabuwar cibiyar koyar da sana’o’i ta Kazaure

0 66

Gwamnatin jihar Jigawa ta bada tabbacin tallafawa sabuwar cibiyar koyar da sanaoi da bankin access tare da hukumar masu yiwa kasa hidima suka gina a garin Kazaure.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bada wannan tabbaci a lokacin bikin mika cibiyar ga babban daraktan hukumar masu yiwa kasa hidima ta kasa a garin Kazaure.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban sakataren kudi da mulki a ofishin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri yace za a tura jamian tsaro domin kula da cibiyar domin gudun barnatarwa daga batagari.

Yace akwai alaka mai kyau a tsakanin gwamnatin jiha da hukumar masu yiwa kasa hidima wadda ya yi fatan hakan zai cigaba.

Gwamnan ya hori sauran jihohi dasu rungumi tsarin koyarda matasa sanaoin dogaro da kai.

A nasa jawabin babban daraktan hukumar masu yiwa kasa hidima Birgediya janar Shuaibu Ibrahim yace cibiyar zata tallafawa matasan jihar Jigawa wajen koyan sanao’in dogaro da kai domin su kasance masu iya sanaar sarrafa na’ura mai kwakwalwa da sauran sanaoin dogaro da kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: