Yan bindiga a jihar Zamfara sun sake garkuwa da wani attajirin dan kasuwa bayan ya tsere

0 102

Yan bindiga a jihar Zamfara, sun sake garkuwa da wani attajirin dan kasuwa, Aminu Jangeme, shekara daya bayan ya tsere daga hannunsu.

An yi garkuwa da dan kasuwar wanda aka fi sani da Sarki a kauyensa tare da wasu mutane shida a shekarar 2020.

Manema Labarai sun rawaito cewa yayin da ake tattauna batun biyan kudin fansarsa, sai Allah ya bashi sa’ar tserewa sannan ya gudu garin Gusau tare da iyalinsa.

An kuma rawaito cewa Alhaji Aminu Jangeme ya dawo kauyen ba tare da ya san cewa ‘yan bindigar na nan suna nemansa ba.

An tattaro cewa sun sake yin garkuwa da shi a gonarsa da ke hanyar Gusau-Dansadau tun ranar Alhamis da ta gabata.

Yayansa, Mallam Adili, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya nuna tsoron cewa watakila maharan ba za su sake shi ba a wannan karon saboda sun dade suna nemansa tun bayan da ya tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: