Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala sama da kashi 95 cikin 100 na ayyukan data gada daga gwamnatocin da suka gabata wadanda kudinsu ya haura naira miliyan dubu 96

0 53

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala sama da kashi 95 cikin 100 na ayyukan data gada daga gwamnatocin da suka gabata wadanda kudinsu ya haura naira miliyan dubu 96.

Darakta Janar na hukumar tantance ayyukan kwangila ta jihar Jigawa, Ado Hussaini, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse.

Shugaban hukumar ta due process ya bayyana cewa sauran ayyukan da wannan gwamnatin ta gada kuma yanzu ake kokarin kammalawa sun hada da titin Limawa zuwa Warwade, da aikin titunan cikin garin Dutse kashi na daya dana biyu, da karasa aikin titin kasuwar duniya ta Maigatari, da aikin titin zuwa gidajen ‘yan majalisu dake Dutse sai kuma aikin daga darajar wasu ayyukan ruwan sha guda 34 wadanda gwamnatin Ibrahim Saminu Turaki ta fara ta yi watsi dasu.

Ado Hussaini ya kuma bayyana cewa ya zuwa wannan lokaci gwamnatin jihar jigawa ta kuma kammala biyan kashi biyu cikin uku na bashin kudaden da ‘yan kwangila ke bin gwamnatocin Saminu Turaki da Sule Lamido wanda ya kai kusan naira miliyan dubu 4.

Yace da yardar Allah, Gwamna Badaru Abubakar zai kammala dukkan ayyukan da ya gada a jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: