Labarai

Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Jigawa JISEPA ta kaddamar da aikin yashe magudanan ruwa a Dutse na tsawon makonni biyu

Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Jigawa JISEPA ta kaddamar da aikin yashe magudanan ruwa a Dutse na tsawon makonni biyu.

Mukaddashin manajan daraktan hukumar, Injiniya Lawan Ahmed Zauma ne ya kaddamar da aikin a titin Hakimi street dake Dutse.

Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Ahmed Zauma ya ce manufar aikin shine tabbatar da tsaftace birnin Dutse.

Injiniya Ahmed Lawan Zauma ya bukaci al’umma da su tallafawa jami’an hukumar ta hanyar zubar da shara a guraren da hukumar ta tanadar.

A nasa jawabin, darakta mai kula da ayyukan hukumar, Injiniya Muktar Muhammad Usman, ya bayar da tabbacin zasu sanya ido domin aiki ya gudana ciki nasara tare da yi kira ga kungiyoyin ‘yan kasuwa da masana’antu da su kara kulawa wajen tsaftace wuraren sana’oinsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: