Shugabar Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya, Rhoda Dia, ta ce kimanin kashi 97 cikin 100 na al’ummar Najeriya har yanzu suna amfani da itace wajen dafa abinci da sauran ayyuka.

Rhoda Dia ta bayyana haka ne jiya a wajen wani taron tattaunawa na wuni biyu na masu ruwa da tsaki na kasa kan shigar da harkar noma da amfanin gonaki cikin manufofin kasa kan muhalli a garin Keffi na jihar Nasarawa.

Ta ce sare bishiyoyi domin itacen yana lalata kasa tare da jawo mata matsaloli da dama wadanda ke shafar dorewar muhalli da samar da abinci.

Ta ce akwai bukatar a samo bakin zaren warware wannan dabi’a ta wasu domin rage illar da sare itatuwa ke haifarwa wajen samun abinci a nan gaba.

A cewarta, Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da aiwatar da ayyukan tabbatar da wadatar abinci a jihohi bakwai da suka hada da Jigawa, Kano, Katsina, Benue, Nasarawa, Gombe, da Adamawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: