Hukumar EFCC ta samu umarnin kotu na tsare Akanta Janar na tarayya Ahmed Idris na karin wasu kwanaki

0 39

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta samu umarnin kotu na tsare Akanta Janar na tarayya Ahmed Idris na karin wasu kwanaki.

Wani jami’in hukumar da bai so a ambaci sunan sa ba, ya bayyana cewa sashin shari’a na hukumar ne ya tabbatar da hakan cikin sa’o’i 24 bayan an kama Ahmed Idris a Kano.

Duk da cewa jami’in hukumar bai bayyana kotun da aka samu umarnin ba, amma ya bayyana cewa sun dogara da umarnin a ci gaba da tsare shi har sai sun kammala bincikensu.

Da aka tambaye shi lokacin da za a sake shi, jami’in hukumar ya ce za a iya gurfanar da Ahmed Idris a kotu a kowane lokaci daga yanzu.

Ya kara da cewa wasu kadarorin da ke da alaka da shi a Abuja, Legas da kuma Kano za a iya kwace su na wani dan lokaci, yana mai cewa hukumar za ta kuma matsawa gwamnatin tarayya ta kwace su gabadaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: