Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaucewa cinkoson abeben hawa a karamar hukumar Gwaram

0 91

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaucewa cinkoson abeben hawa a akan hanyar da ta hada Kano da Jihohin Arewa Maso Gabas, bisa fargabar da mutane suke da ita akan wata babbar Gada, sakamakon mamakon ruwan sama.

Gadar ita ce ta hada karamar hukumar Gwaram ta nan jihar Jigawa da kuma Jihohin Bauchi, Gombe da Kuma Taraba.

Cikin wata Sanarwa da Kakakin Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, wato Habibu Nuhu Kila, ya rabawa manema labarai, sanarwar ta ce gwamnatin jihar Jigawa ta umarci matafiyan su nemi mafita, domin bawa gwamnati damar yin aiki akan gadar.

Sanarwar ta rawaito cewa Habibu Nuhu Kila, ya umarci masu manyan motoci, suyi amfani da babbar hanyar Gwaram zuwa Kari wacce ta hada Jihohin har zuwa lokacin da za’a kammala aiki akan gadar.

Kazalika, Injiniyan Kamfanin Alren Construction company, wanda yake aiki a kan gadar, Mista Tonnous Finianos, ya fadawa manema labarai cewa ambaliyar ruwa ce tayi sanadiyar karyewar gadar data shafe tsawon shekaru 40.

Leave a Reply

%d bloggers like this: