Gwamnatin Jihar Jigawa ta samar da cibiyoyi fiye da 300 domin ilimantar da al’umma ayyuka da kuma koyarwar addinin Musulunci.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ne ya sanar da haka a jiya lokacin rufe musabakar ilimin addinin Musulunci ta Jiha karo na hudu wadda aka gudanar a kwalejin fasaha dake Dutse.

Gwamnan ya yi kira ga al’umma da su cigaba da yin addu’oi domin kawo karshen matsalolin tsaro da suke addabar kasar nan.

Gwamna Badaru Abubakar ya kuma yabawa kwamatin shirya musabakar, inda yayi alkawarin bayar da dukkanin hadin kai da goyon baya domin kaiwa ga nasara.

Daga bisani an raba kyaututtuka ga wadanda suka zama zakaru da suka hadar da babura da na’urorin sanyaya ruwa da talabijin da sauran kayayyaki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: