Matsalar rashin tsaron da ya addabi Najeriya ya kusa zuwa karshe – Shugaba Buhari

0 103

Shugaba Muhammadu Buhari yace matsalar rashin tsaron da ya addabi Najeriya ya kusa zuwa karshe domin kayan aiki sun kusa shigo wa hannu.

Shugaba  Muhammadu Buhari yace jiragen Super Tucano da wasu jiragen yaki masu saukar ungulu da gwamnatinsa ta saya daga Amurka suna hanya.

 Manema labarai sun ce shugaban kasar ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, 2021, yayin da ake yin taro na majalisar dinkin Duniya.

Buhari ya shaida wa jakadar Amurka a majalisar dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, cewa gwamnatinsa tana kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: