An kama kwantenoni 185 na magungunan da ba a yi musu rajista ba a jihar Jigawa

0 70

Hukumar Kwastam ta Kano da Jigawa a jiya ta mikawa Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) kwantenoni 185 na magungunan da ba a yi musu rajista ba.

Kwanturolan rundunar, Suleiman Umar Pai, ya mika magungunan ga Coordinator na NAFDAC na jihar Kano, Shaba Muhammad.

Ya ce an kama miyagun kwayoyi daga hannun masu fasa kwauri daga watan Yuli zuwa yau.

Umar Pai ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai ga wannan hidimar, ta yadda za kare tattalin arzikin daga masu fasa kwauri da kuma tsare lafiyar mutane.

A nasa jawabin, mai kula da NAFDAC ya yaba da hadin kan da ke akwai tsakanin hukumarsa da hukumar kwastam wajen magance hada-hadar miyagun kwayoyi a kasar.

Ya kuma shawarci mutane da su rinka kula da kantin magani da aka yi wa rajista kadai, don gujewa shan magungunan da suka lalace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: