Mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce wasu daga cikin mutanen da ke zagin shugaban kasar na komawa Aso Rock a bainar jama’a don cin abincin dare.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya fadi haka ne yayin da yake tsokaci kan dawowar Femi Fani-Kayode zuwa jam’iyyar APC.

Fani-Kayode na shan suka tun makon da ya gabata lokacin da Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen Babban Taron APC na Kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya gabatar da shi ga Buhari a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

‘Ya’yan jam’iyyar APC da na PDP sun yi ta zagin sa kan sauya sheka.

A cikin makalrsa ta mako-mako, Adesina ya ce Buhari mutum ne mara riko, kuma yadda ya karbi Fani-Kayode ya nuna hakan.

Mai magana da yawun shugaban kasa ya ce banda Fani-Kayode, Buhari ya yi liyafa da cin abinci tare da wasu mutanen da ke la’antarsa a bainar jama’a.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: