Wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa a Sudan Ta Kudu, sun jima suna bushasha da dukiyar kasar.

Kwamitin, wanda ke a matsayin na kare hakkin dan adam a Sudan ta Kudun ya ce ya samu kwararan shaidu da ke nuna yadda wasu ‘yan siyasa da makusantan gwamnati suka kasafta miliyoyin daloli a tsakaninsu tun daga shekarar 2018.

Rahoton ya ce yawan kudaden da aka sacen ya kai dalar Amurka miliyan 73.

Kwamitin yace wannan adadi kadan ne daga cikin adadin kudin da aka sace.

Rahoton ya ce wannan matakin cin hanci da rashawa yana tauye hakkin dan adam da rashin tsaro a kasar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: