Gwamnatin jihar Jigawa za ta hada gwiwa da wata cibiyar kasar Koriya ta Kudu, da ta kware kan binciken kimiyyar tsirrai da aikin gona.

Gwamnan jiha Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci cibiyar tare da jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, Alhaji Ali Mohammed Magashi.

Jami’in cibiyar ya karbi bakuncin gwamnan da jakadan, inda ya zagaya da su rangadi zuwa cibiyar ta bincike, tare da ziyartar wasu daga cikin gonakan da ake gudanar da binciken kimiyyar tsirrai da aikin gona.

Bayan kwashe sa’o’i ana zagaye da tattaunawa, gwamnan ya bai wa cibiyar tabbacin cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da cibiyar, domin cin gajiyar binciken kimiyyar tsirrai da aikin gona a nan jihar Jigawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: