Shugaban hukumar kiyaye hadura ta kasa, Boboye Oyeyemi, ya kaddamar da kyamarar makalawa a jiki domin sanya ido da kula da aiki, da nufin inganta ayyukan hukumar a fadin kasarnan.

A wajen kaddamarwar da aka gudanar a Abuja a hukumance, Oyeyemi yace hakan zai inganta tabbatar da gaskiya da amana a ayyukan hukumar a fadin kasarnan.

Ya kara da cewa an fito da kyamarar bisa la’akari da bukatun al’umma, wanda shine akan gaba, kasancewar hukumar ta dauki gabarar sanya jami’anta su zamto masu himma a ayyukansu.

Oyeyemi ya kuma ce hakan ‘yar manuniya ce ta amfani da fasaha da nufin dakile matsalolin da ake fuskanta a ayyukan jami’an hukumar tare da jajircewa wajen magance dukkan kalubalen da hukumar ke fuskantar wajen sauke nauyin dake wuyanta.

A cewarsa, kyamarar makalawa a jiki tana da muhimmancin gaske, kasancewar tana da alfanu dayawa ga hukumar da ma tsaron kasa baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: