Magatakarda hukumar jarabawar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce jerin matakan da aka bullo da su don dakile yin magudi da aikata satar amsar jarrabawa sun fara haifar da da mai ido.

Oloyede ya bayyana hakan ne a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin da yake gabatar da jawabi.

Oloyede ya ce wasu daga cikin matakan na komfuta, an samar da su ne don cimma burin hukumar na kakkabe aikata ba daidai ba da sauran nau’ikan rashin bin doka.

A cewarsa, irin wannan matakan sun hada da amfani da Lambar Shaidar Zama Dan Kasa ta NIN, da sanya ido kan rajistar jarabawa da kuma yin amfani da manhajar samar da guraben karatu a manyan karatu.

Shugaban na JAMB ya ce ya fara kokarin kawo sauyi ga ayyukan hukumar ta hanyar kula da jin dadi da walwalar ma’aikata, da nufin karfafa musu gwiwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: