Gwamnatin jihar Jigawa zata hada gwiwa da wani kamfani a kasar Koriya ta Kudu domin inganta noman shinkafa da ridi

0 167

Gwamnatin jihar Jigawa zata hada gwiwa da wani kamfani a kasar Koriya ta Kudu domin inganta noman shinkafa da ridi a jiharnan.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana hakan yayin ganawa da jami’an kamfanin a Koriya ta Kudu.

Gwamnan wanda ke tare da jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, Ali Magashi, ya gana da shugaban kamfanin, Chang Donghee kuma sun tattauna akan muhimman batutuwa da suka shafi cigaban jihar Jigawa tare da niyyar hadin gwiwa da kamfanin wajen nemo hanyoyin zamani na noman shinkafa da noman ridi a nan Jigawa.

A cewar gwamnan, gwamnatin jihar Jigawa za ta dauki nauyin kamfanin zuwa jihar Jigawa domin su yi aiki a bangarorin noma, kiwon lafiya da ilimi a jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: