Mabiya addinin Kirista, ciki har da malamai, sun ziyarci Musulmai zuwa wajen bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, jiya a Kaduna.

Mabiya addinan biyu, wadanda suka hadu a filin wasa na Rachers Bees da ke birnin, sun ce sun yi hakan ne da nufin karfafa dankon zumunci da inganta al’adu tare.

Babban limamin cocin Christ Evangelical dake Sabon Tasha, Fasto Yohanna Buru, wanda ya jagoranci tawagar Kiristoci, ya ce sun je wajen ne don murnar haihuwar annabi.

Ya lura cewa a matsayinsa na jakadan zaman lafiya kuma malamin addinin Kirista, shiga cikin Musulmai baya canza kasancewarsa Kirista.

Ya bukaci mabiya addinan biyu da su yi amfani da wannan lokaci don inganta juriya, soyayya, hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Malamin na Kirista ya kuma yi kira ga dukkan Musulmai da su yi amfani da lokacin Maulud don yin addu’ar neman taimakon Allah don kawo karshen matsalolin da ke dagula zaman lafiyar kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: