Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon murnar cikarsa shekaru 87 a duniya.

Shugaban, a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Garba Shehu, ya taya tsohon shugaban kasar da iyalansa murnar da fatan karin lafiya da karfin gwiwa don ci gaba da yiwa kasa hidima.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wata ziyarar aiki ta wuni biyu zuwa Najeriya daga jiya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa wacce babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu, ya fitar a jiya.

Tare da rakiyar Uwargidan Shugaban kasa, Emine Erdogan, Shugaba Erdogan ya shigo daga Angola, sannan zai tashi zuwa Togo a karshen ziyarar tasa.

A yayin ziyarar, ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su duba yarjejeniyoyin fahimtar juna tsakanin kasashen.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: