Gwamnatin jihar Kaduna ta sake bayyana cewa ƴan bindiga sun sake kashe mutane 9 da kuma raunata mutum 2

0 99

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ƴan bindiga sun kashe mutane 9 da kuma raunata mutum 2 a wasu hare-haren da aka kai a Ƙananan Hukumomin Chikun da Zaria da Zangon Kataf.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Mista Samuel Aruwan ya fitar, tace an kashe mutum uku yayin da ƴan bindiga suka yi wa garuruwan Buruku da Udawa tsinke.

Haka kuma a yankunan Yola da Kadi da ke Ƙaramar Hukumar Chikun, ƴan bindigar sun kashe mutum guda da raunata ɗaya.

Yan bindigan sun sake kashe mutum biyu a ƙauyen Sako da ke Zangon Kataf, haka kuma an gano gawarwakin mutum biyu a yankunan Kurfi da Magamiya dake Zangon kataf..

Haka ma a Ƙaramar Hukumar Zaria, an kashe mutum ɗaya a ƙauyen Saye.

Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya nuna ɓacin ransa kan wannan lamari tare da addu’a ga waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka jikkata su samu sauƙi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: