Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani asibiti mai zaman kansa dake kauyen Rimi na karamar hukumar Sumaila

0 85

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani Asibiti mai zaman kansa, Mai Suna Kabir Global Clinic wanda yake kyauyen Rimi na karamar hukumar Sumaila ta jihar saboda an bude shi ba bisa ka’ida ba.

Shugaban Hukumar Lura da Asibitoci Masu Zaman Kansu ta Jihar KANO Dr Usman Aliyu, shine ya bayyana hakan, inda ya ce hukumar ta gano Asibitin ne biyo bayan ziyarar aiki da take kaiwa a jihar.

Sanarwar ta ce hukumar ta kuma rufe wasu Asibitoci masu zaman kansu 3 Habeeba Salam Clinic in Garko Local Government, Gidan Ruwa Clinic in Wudil Local Government, and Ali Alkali Clinic in Takai Local Government Areas, bisa samun da laifin yin Tiyata ba tare da samun kwararrun Likitoci da Ma’aikatan Jinya ba.

Shugaban Hukumar ya ce sun rufe Cibiyoyin har sai Asibitocin sun dauki kwararrun Likitoci bayan hukumar ta kammala bincike.

Kazalika, ya ce hukumar zata gurfanar da mas Asibitocin a gaban Kotu domin girbar abinda suka shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: