Majalisar Zartarwa ta Jihar Yobe ta amince da gina Cibiyar Keɓewa mai gadaje 200 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe

0 182

Majalisar Zartarwa ta Jihar Yobe ta amince da gina Cibiyar Keɓewa mai gadaje 200 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu a kan kuɗi Naira biliyan 7 da miliyan 22 da dubu 754.

Kwamishinan Yada Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu, Alhaji Abdullahi Bego ne ya sanar da hakan a jiya a karshen taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta a Damaturu, babban birnin jihar.

A cewar Mista Bego, kudin da aka amince da shi zai dauki nauyin wasu ayyukan kiwon lafiya da gina tituna a cikin jihar da kuma filin jirgin saman Yobe Cargo da ake kan ginawa.

Ya kuma ce Majalisar ta amince da kashe naira miliyan 288 da dubu 998 don gina titin mai tsawon kilomita 1.5 da magudanar siminti mai tsawon kilomita 3.0 ta hanyar aiki kai tsaye a kwalejin koyan aikin jinya da ungozoma ta Dr Shehu Sule, Damaturu.

Kwamishinan ya kara da cewa an amince da jimillar Naira miliyan 169 don gyaran hanyar Kaliyari zuwa Bayamari da tare da gyaran hanyar Jakusko-Garin Alkali akan kudi Naira miliyan 219 da dubu 698.

Sanarwar ta ce Majalisar ta kuma amince da kashe Naira biliyan 1 da miliyan 225 da dubu 632 don sake yin wasu ayyuka a kan aikin Kasuwar zamani na Nguru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: