Ba za muyi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya ci amanar da aka dora

0 101

Ma’aikatan fadar shugaban kasa dake Abuja, ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya ci amanar da aka dora masa yayin gudanar da aikinsa.

Babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar ne ya yi wannan gargadin yayin kaddamar da sashin yaki da cin hanci da rashawa na fadar, da aka yi jiya a Abuja.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka ta kasa (ICPC) ce ta kaddamar da sashin.

Tijjani Umar ya taya ma’aikatan sashin murna, yana mai cewa musamman aka zabo su daga cikin ma’aikatan fadar shugaban kasa bisa nagartar su da kokarinsu wajen gudanar da aiki.

Ya kara da cewa yana sa ran za su taimaka wa sashen wajen dora shi bisa turbar cigaba ta hanyar bayar da shawarwari, da bayar da rahoto idan ya zama dole, tare da zartar da doka da hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: