Karamar hukumar Rano ta jihar Kano ta kafa dokar hana maza da mata haduwa domin fira da daddare

0 122

Karamar hukumar Rano ta jihar Kano ta kafa dokar ta hana maza da mata haduwa domin fira da daddare.

Karamar hukumar ta ce hakan ya zo ne sakamakon rahotannin da ake samu na ayyukan ash-sha tsakanin ‘yan mata da samari, gami da zawarawa.

Ya ce masoya na iya haduwa da rana ne kawai domin yin fira.

A cewar jami’in yada labarai na karamar hukumar, Habibu Faragai, shugaban karamar hukumar, Dahiru Muhammad, ya sanar da dokar a taron kwamitin tsaro wanda mutanen karamar hukumar da shugabannin gargajiya suka halarta.

Dahiru Muhammad ya ce kwamitin ya jawo hankali game da yawaitar ayyukan badala a karamar hukumar, idan ya kara da cewa hakan ya sanya majalisar karamar hukumar ta fito da sabuwar dokar.

Ya ce an yi dokar ne don tsabtace karamar hukumar daga ayyukan ash-sha da ke faruwa yayin firar dare tsakanin maza da mata.

Shugaban karamar hukumar ya umarci hukumar Hisbah da ta tabbatar da bin dokar tare da kama wadanda suke take ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: