Gwamnatin Jihar Katsina ta raba babura dubu 8 na bashi ga malaman firamare

0 98

Gwamnatin Jihar Katsina tace ta raba babura dubu 8 na bashi ga malaman firamare da kananan sakandire a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.

Shugaban hukumar ilimi matafin karfo ta jihar, Lawal Buhari Daura, ya sanar da haka jiya a Katsina lokacin da yake karbar matasan labaran internet na jam’iyyar APC a ziyarar aikin da suka kai.

Buhari-Daura yace baburan zasu taimaka wajen saukaka zirga-zirgar Malamai domin baiwa dalibai ilimin da ake bukata.

Yace hukumar ta sayi karin babura 15 da motaci biyu domin ziyarar gani da ido zuwa makarantu, wadanda zasu karade kananan hukumomi 34 na jihar.

Dangane da walwalar malamai, shugaban hukumar yace malaman jihar basa bin gwamnatin jihar bashin karin girma da na albashi da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: