Babbar kotun jihar Adamawa ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum daya kashe matarsa da danta

0 242

Babbar kotun jihar Adamawa ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum dan shekara 40 mai suna Bangos Adams, bisa laifin kashe matarsa da danta.

Mai shari’ah Fatimah Ahmed Tafida ta bayar da umarnin cewa a rataye Bangos Adams a wuyansa har sai ya mutu.

Fatimah Tafida tace masu gabatar da kara sun gamsar da kotun cewa Bangos Adams yana da laifi a tuhumarsa da ake yi, shiyasa aka yanke masa hukunci.

Bangos Adams wanda ya fito daga kauyen Janjaba a yankin karamar hukumar Gumbi ta jihar Adamawa, an gurfanar da shi kuma an same shi da laifin kashe matarsa Regina Bangos da danta Revelation James.

An rawaito cewa wanda aka yankewa hukuncin, wanda kuma manomi ne, tunda farko a gurfanar da shi a gaban kotun bisa kashe matarsa ta hanyar bugun kanta da gatari da kuma sare kan danta da adda, lamarin da ya jawo mutuwarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: