An harbe wasu mutane biyu da ake zargin masu satar mutane ne a jihar Taraba yayin da suka je karbar kudin fansa

0 75

An harbe wasu mutane biyu da ake zargin masu satar mutane ne, a lokacin da suka je karbar kudin fansa a garin Sabongida da ke karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba.

An rawaito cewa, wadanda ake zargin sun sace wani tsoho mai suna Alhaji Gambo.

Masu garkuwa da mutanen wato Sani da Musa, sun umarci iyalan Alhaji Gambo, su kai kudin fansa inda wani wuri, don haka aka shaidawa ‘yan kato da gora inda suka je dajin sukai musu kwantan bauna.

Masu satar mutanen dauke da muggan makamai, sun isa wajen, ba tare da sun san an yi musu kwantan bauna ba, inda ‘yan kato da gorar suka bude musu wuta a lokacin da suka sunkuya domin daukar kudin.

An samu kubatar da Alhaji Gambo, da aka zo biyan kudin fansar sa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Abdullahi Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai kara cewa komai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: