Ana ci gaba da samun sabbin mutane dake kamuwa da cutar corona a Najeriya

0 84

Ana ci gaba da samun sabbin mutane dake kamuwa da cutar corona a kasar nan, bayan da a jiya aka samu sabbin mutane 505 da suka kamu da cutar a jiya Talata.

Hukumar dakile bazuwar cuttuttuka ta kasa NCDC ta wallafa cewa sabbin wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga Jihohin kasar nan 13 da babban birnin tarayya Abuja.

Jihar Legas wanda itace jihar da tafi yawan wandada suka kamu da cutar ansami sabbin mutane 273 sai jihar Rivers da mutane  83, sai kuma jihar Oyo mutane 45.

Sauran Jihohin sunhada Ondo (22), Cross River (18), Kaduna (13), Ogun (10), Gombe (10), FCT (8), Ekiti (7), Delta (6), Bayelsa (3), Edo (2), and Niger (1).

NCDC ta kara da cewa a jiyan an sallami mutane 85 bayan sun warke daga cutar.

Hukumar dakile bazuwar cuttuttuka ta kasa ta kara da cewa mutum 3 sun rigamu gidan gaskiya a jiyan wanda ya maida yawan wadanda suka mutu sanadiyyar wannan cutar a kasar nan zuwa 2,163.

Kawo yanzu dai kimainin mutane 175,264 aka tabbatar da cewa sun kamu da wannna cutar tin bayan bullarta yayin da mutane 165,122 aka sallamesu bayan sun warke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: