Gwamnatin Jihar Neja tace tsagin kungiyar ISWAP da mayakan Boko Haram suna kafa sansanoni a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane, ya sanar da haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Minna, babban birnin jihar.

Ahmed Matane yace yan fashin daji na hada kai da mayakan domin shigar da wasu mazauna kauyuka a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Sakataren gwamnatin ya lissafa kauyukan da yan bindigar suka shiga da suka hada da Shukuba, Koki, Kusare da Madaka.

Ahmed yace kungiyar na tabbatarwa da mazauna kauyukan samun tsaro amma sun nemi su watsar da karatun boko da dokokin gwamnati.

Sakataren gwamnatin jihar yace hadin kai tsakanin ‘yan fashin daji da Boko Haram ya kara yawan hare-hare akan mazauna kauyukan da su ji ba, ba su gani ba, a ‘yan kwanakinnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: