Gwamnatin jihar Yobe ta ce zata bawa Almajirai dubu 12 kayan sallah da abinci domin bikin babbar sallah ta bana.

Shugaban hukumar bada agajin gaggauwa ta jihar SEMA Dakta Muhammadu Goje ne ya bayyana hakan cikin wani sako daya rabawa manema labarai a birnin Damaturu dake jihar.

A cewarsa zasu raba abinci da kayan sawa ga Almajirai da suke kimanin tsangayoyi 240 na kananan hukumomi 7 a jihar.

Ya kara da cewar ciyarwa na daya daga cikin kudirin gwamnatin Mai Mala Buni wajan samar da abinci ga masu karamin karfi

Anasa bangaren wani malamin Tsangaya mai suna Malam Modu Goni, yace, shi da dalibansa na cikin farin ciki marar misaltuwa,  tare da kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni akan suyi amfani da wannan lokacin wajan taimakawa masu karamin karfi a fadin kasar nan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: