Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da fiye da naira biliyan 20 domin kammala wasu manyan ayyuka

0 77

Majalisar dokoki ta jihar Jigawa ta amince da kwaryakwaryan kasafin kudi na fiye da naira biliyan 20 da miliyan 436 da bangaren gwamnati ya gabatar wa majalisar dokoki domin tabbatar da kammala wasu manyan ayyuka a fadin jiha.

Kafin hakan dai a ranar 12 ga watan Yuli na wannan shekara Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya bada rahoton cewa gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya aike da kwarya kwarya kasafin kudin da ya kai naira biliyan 18 da miliyan 88 domin amincewa.

Ayyukan da za’akammala ko farawa da wadannan kudaden sunhada bunkasa masana’antu, samar da ruwan sha, inganta fannin noma da kuma jinkan matan dake fadin jihar nan.

Yayin gabatar da kasafin ga zauran majalissar jiha shugaban kwamtin Muhammad Abubakar, dan majalissa ne mai wakiltar karamar hukumar Maigatari yayi kira ga sauran mambobin majalissar da su bada hadin kai wajan tabbatar da wannan kasafin.

Hakannne yasa kwamitin suka amince, Ya kara da cewa majalisar ta yi karin naira miliyan dubu 2 da miliyan 444 domin ci gaba da gudanar da ayyukan mazabu da ‘yan majalisar suke gudanarwa a mazabunsu kai tsaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: