Wasu yan bindiga sunyi garkuwa da uwargidan Tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama

0 83

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sunyi garkuwa da uwargidan Tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama Alhaji Ahmed Yahaya Marke

yan bindigar da adadin su ya kai 10 sun farwa gidan Tsohon shugaban karamar hukumar ne dake Marke da misalin 10 na safiyar yau laraba.

Uwargidan Tsohon shugaban karamar hukumar da aka bayyana sunan ta da Hajiya Fatima, itace matarsa ta farko wato uwargidan sa.

Guda cikin yaran matar da akayi garkuwa da ita mai mai suna Aliyu Ahmed shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan Telelbijin na channels, inda yace masu garkuwar sunzo ne akan babura daban daban.

Ya kara da cewa kawo yanzu am tintibi wasu daga cikin yan’uwansa akan maganar sakin Hajiyar, amma kawo yanzu basu nemi a basu kudin fansa ba.

Anasa bangaren Jami’in yada labarai na hukumar yansandan jihar nan ASP Lawan Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Tare da tabbbatar da cewa yanzu haka hukumar yansadan jihar Jigawa ta hada kai da yan Bijilanti da Mafarauta domin gano inda bata garin suke

Leave a Reply

%d bloggers like this: