Labarai

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sauke sarakuna biyu da wani hakimi bisa zargin taimakawa ayyukan ‘yan fashin daji dake addabar kauyukan jihar

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sauke sarakuna biyu da wani hakimi bisa zargin taimakawa ayyukan ‘yan fashin daji dake addabar kauyukan jihar.

Sarakunan da aka sauke sune Sarkin Zurmi, Alhaji Abubakar Atiku, da Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar.

Hakimin Birnin Tsaba, Alhaji Sulaiman Ibrahim, shi ma an sauke shi.

Kwamishinan labaran jihar, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara, shine ya sanar da sauke sarakunan ga ‘yan jarida, jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwar jihar.

Majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin bincike mai wakilai 6 wanda gwamnatin jihar ta kafa da nufin bincikar zargin da ake yiwa sarakunan na hannu a ayyukan ‘yan fashin daji a jihar.

Gwamnatin jihar tun a baya ta dakatar da sarakunan da aka sauke bisa yawaitar zarge-zargen hannu a ayyukan ‘yan fashin daji a jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: