Gwamnatin kasar Burkina Faso tace an samu gawarwakin sojoji 11 tare da batan fararen hula 50 biyo bayan wani hari da masu ikirarin jihadi suka kaddamar

0 60

Gwamnatin Kasar Burkina Faso tace an samu gawarwakin sojoji 11 tare da batan fararen hula 50 biyo bayan wani hari da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kaddamar akan wani ayarin motoci.

An bayar da rahotan cewa wasu mutane 28 cikin har da sojoji 20 sun ji rauni a harin na ranar Litinin kuma ana cigaba da aikin neman wadanda suka bata.

Motocin wadanda ke samun rakiyar sojoji na dauke da kayan masarufi zuwa mutanen dake zaune a arewacin kasar.

Kwanton baunan ya biyo bayan wani hari akan wasu ayarin motocin dake samun rakiyar sojoji a ranar Lahadi wanda ya raunata mutane 4.

Gwamnatin sojan dake mulkin Burkina Faso ya kwace madafun iko yayin wani juyin mulki a watan Janairun da ya gabata, tare da alkawarin kawo karshen tada kayar baya wanda ya jawo mutuwar dubban mutane tare da raba wasu mutane miliyan biyu da gidajensu tun daga shekarar 2015.

Leave a Reply

%d bloggers like this: