Akalla mutane 23 ne aka ruwaito sun mutu sannan wasu dubu 116 da 84 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Benue

0 81

Akalla mutane 23 ne aka ruwaito sun mutu sannan wasu dubu 116 da 84 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Benue.

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Benue Mista Emmanuel Shior ne ya bayyana hakan jiya a wani taron manema labarai a Makurdi babban birnin jihar domin kaddamar da rabon kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.

Ya bayyana cewa an samu mace-macen mutane 14 a karamar hukumar Guma, biyu a karamar hukumar Vandekiya, hudu a karamar hukumar Katsina-Ala sannan uku sun mutu a karamar hukumar Agatu.

Emmanuel Shior ya ci gaba da bayyana cewa, adadin gonaki dubu 14 da 40 ne ambaliyar ta lalata yayin da gidaje dubu 4 da 411 suka rushe.

Ya ce mutane dubu 116 da 84 da suka rasa matsugunansu sun fito daga gidaje dubu 12 da 856 a kauyuka 104 cikin kananan hukumomi 11 da abin ya shafa, tare da jikkata mutane 14.

Ya kuma ce hukumar za ta kwashe ‘yan gudun hijirar da suka mamaye wata babbar hanya zuwa wani sansani da aka kebe inda za a samar musu da kayan agaji da tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: