Hukumar asibitin koyarwa ta jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi tace an samo jariri dan kwana 14 a duniya da aka sace daga asibitin a Bauchi

0 46

Hukumar asibitin koyarwa ta jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi tace an samo Jariri Dan Kwana 14 a duniya da aka sace daga Asibitin a Bauchi.

Shugaban Kwamitin bayar da shawarar likitoci na asibitin, Dr Haruna Liman, shine ya bayyana hakan lokacin da yake mika Jaririn ga mahaifiyarsa a Bauchi.

Yace an sace jaririn daga wajen mahaifiyarsa a asibitin, kwanaki 8 bayan ta haihu.

Dr Haruna Liman yace tuni hukumomin tsaro suka kama wata mata da suke zarginta da kitsa satar.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar asibitin za ta inganta tsarin tsaron asibitin tare da sanya karin na’u’rorin tsaro a asibitin.

A nasa jawabin, hakimin garin Bauchi, Nura Jumba, ya bukaci hukumar asibitin da ta inganta tsaron asibitin cikin gaggawa domin dakile aukuwar hakan a gaba.

Da yake mayar da martani a madadin iyalan Jaririn, Shitu Khalid ya bayyana godiya ga hukumar asibitin bisa kokarinta da kuma hukumomin tsaro bisa kwato jaririn.

Leave a Reply

%d bloggers like this: