Hukumar kula da magunguna da kayan abinci ta jihar Yobe ta ce tana kashe kudi naira miliyan 300 a duk shekara kan shirinta na samar da magunguna a kyauta

0 22

Hukumar kula da magunguna da kayan abinci ta jihar Yobe ta ce tana kashe kudi naira miliyan 300 a duk shekara kan shirinta na samar da magunguna a kyauta.

Babban Sakataren Hukumar, Abdulazeez Mohammed ya bayyana haka a wani taron manema labarai jiya a Damaturu, babban birnin jihar.

A cewarsa, shirin ya shafi talakawa marasa galihu da ba za su iya sayen maganin ba.

Ya ce daga shekarar 2020 zuwa yau, hukumar ta kaddamar da wani asusun a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da na biyu da manyan makarantu 336 a fadin jihar.

Matakin, in ji shi, ya magance matsalar karancin magunguna a wajen hukumar, wanda ke wakiltar kashi 8.4 a shekarar 2022 sabanin kashi 12.24 a shekarar 2021.

Ya ce hukumar ta kuma kaddamar da wani gidan ajiyar kayayyaki na shiyya da ke Postiskum, da aka gyara tare da samar da kayan aiki a babban kantin magani a Damaturu da kuma wasu shagunan shiyya guda biyu a Gashua da Nguru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: