Majalisar Dattawa ta umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta kai agajin gaggawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa

0 59

Majalisar Dattawa a jiya ta umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su kai agajin gaggawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa da sauran sassan kasar nan.

Majalisar ta kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa da su ba da gargadin gaggawa ga yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da nufin dakile asarar rayuka da dukiyoyi a yankunan da lamarin ya shafa.

Kudirin Majalisar Dattawa kan haka ya biyo bayan kudirin da Sanata Danladi Abdullahi Sankara mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma ya dauki nauyin, kan mumunan ambaliyar ruwa da ta afku a wasu kauyukan Jihar Jigawa.

Sanata Abdullahi Sankara a cikin kudirin ya koka da yadda sama da gidaje dubu 1 da 500 a masarautun Ringim, Kazaure, Gumel, Dutse da Hadejia a jihar Jigawa suka lalace tare da asarar rayukan mutane kusan 100.

Ya kara da cewa dubban mutane da suka hada da mata da kananan yara sun rasa matsugunansu tare da zama ‘yan gudun hijira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: