Gwamnatin Mulkin Sojin Jamhuriyar Nijar Ta Tsaurara Matakan Bada Takardar Izinin Shiga ƙasar

0 804

Gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Nijar ta tsaurara matakan bada takardar izinin shiga ƙasar wato biza ga wasu ƙasashen turai a matsayin mayar da martani.

A cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 20 ga watan Augustan shekarar 2025, wadda ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare ya sanyawa hannu, gwamnatin sojin ta sanar da ɗaukar matakin da ke a matsayin martani ga tarin matsalolin da ƴan kasarta ke cin karo dasu wajan samun takarda bizar shiga wasu ƙasashen Turai.

Sanarwa ta ce duk da gargadin da ta sha aike wa offisohin jakadancin ƙasashen na Turai a Nijar na ganin sun sahalewa ƴan ƙasarta samun takardar bizar shiga ƙasashen su lamarin ya ci tura.

Ƙasashen Turai da wannan matakin ma’aikatar diflomasiyyar Nijar ya shafa sun haɗa da Italiya da Netherlands, Jamus, Belguim da Ingila sai kuma Northern Island, waɗanda ta ce daga yanzu ƴan ƙasashen su za su iya nema takarda bizar shiga Nijar ne a offishoshin jakadancinta da ke Geneva da Moscow da kuma Turkiya.

Sai dai sanarwar ta amince wa offishin jakadancin Nijar a Brussels da ya rika bada Biza ga jami’an gwamnatoci da kuma manyan ma’aikata.

Leave a Reply