Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Horas Da ‘Yansandan Cikin Al’umma Dubu 25

0 160

Mai bawa shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina, yace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta horas da ‘yansandan cikin al’umma dubu 25 a kwalejojin ‘yansanda a fadin kasarnan.

Femi Adesina, cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, yace ayyukan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari sun taimaka sosai a dukkan bangarorin cigaban kasa.

Fadar shugaban kasar a ranar Lahadi cikin wani rubutu na musamman a wata takarda mai shafi 90, ta lissafa nasarorin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari cikin shekaru 8 da suka gabata.

Femi Adesina yace ‘yansandan cikin al’umma za suyi aiki a matsayin masu shiga tsakanin ‘yansanda da al’ummarsu tare da taimakawa wajen tattara bayanan sirri.

Yace gwamnatin, a watan Yunin 2019, ta sanya hannu akan kudirin dokar asusun ‘yansanda wanda ya kafa hukumar asusun ‘yansanda.

Femi Adesina yace an yi hakan domin samar da kudaden sayan kayan aikin ‘yansanda da inganta jin dadinsu.

Leave a Reply