Nasarorin Da Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Samu Wajen Magance Matsalar Tsaro

0 72

Fadar shugaban kasa ta bayyana irin nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu wajen magance matsalar tsaro tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, a cikin wata takarda mai shafuka 90 da ya fitar jiya a Abuja, ya ce ayyukan na shugaban kasa sun yi tasiri sosai kan sauye-sauyen da ake samu a hukumomin tsaro.
Ya ce Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta kaddamar da sabbin sansanoni 16 a fadin kasarnan, da samar ingantaccen fasfo na intanet wanda kuma ya ke da aiki na tsawon shekaru 10.
A halin da ake ciki kuma, a shekarar 2021 da 2022, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama masu safarar miyagun kwayoyi kimanin dubu 24, ciki har da diloli 29.
Fadar shugaban kasar ta kara da cewa hukumar ta tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifuka sama da dubu 3 da 400.
Har ila yau, Femi Adesina ya ce a shekarar 2020 Shugaba Buhari ya yi wa fursunoni dubu 2 da 600 afuwa a fadin kasar nan a wani bangare na sake fasalin bangaren shari’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: